September 4, 2020 By Adamu Abubakar 0

HANYOYI GUDA TAMANIN (80) DA SUKE KUBATAR DA MUTUM DAGA WUTA

Fitowa ta 0️⃣4️⃣

*RAYUWA TARE DA AL-ƘUR’ANI*

Dukkan wanda ya tozarta al-Ƙur’ani kuma ya bashi baya ya zamto ba shi da alaƙa mai kyau da al-Ƙur’ani, to tabbas al-Ƙur’ani zai zama mai shaida a kansa kuma ɗaya ne daga cikin hanyoyin halaka da shiga azaba, Allah Ta’ala Ya tsare mu.

Allah Ta’ala Ya ce: *”Lallai waɗanda suke karanta littafin Allah kuma su ka tsaida salla kuma suka ciyar daga abun da muka azurta su a fili da ɓoye, su na fatan wani kasuwanci wanda babu faɗuwa”*. Suratu Faaɗir 29.

Sannan Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce: *”Ku karanta al-Ƙur’ani domin zai zo ranar al-Ƙiyama ya na mai ceto ga ma’abotansa”*. Sahih Muslim 804.

*AL-ƘUR’ANI MAI CETO NE DA SHAIDA AKAN MA’ABOCINSA*

Jabir ɗan Abdullahi, Radhiyallahu anhu, ya ce: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce:

*”Al-Ƙur’ani mai ceto ne kuma wanda ake baiwa ceto ne sannan mai shaida ne kuma mai gaskiya – a shaidar shi-, duk wanda ya sanya al-Ƙur’ani a gabansa, to zai jagorance shi zuwa Aljanna, haka nan duk wanda ya sanya shi baya gare shi, to zai ja shi zuwa wuta”*. Hadisi ne ingantacce wanda Ibn Hibban ya fitar da shi a Sahih ɗinsa 124 sannan Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani ya inganta hadisin a cikin Sahih al-Jami’ 4443.

A wani hadisin na Abdullahi ɗan ‘Amru, Radhiyallahu anhumaa, Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, cewa ya yi: *”Za a ce da ma’abocin al-Qur’ani – a ranar al-ƙiyama-: karanta ka hau kuma ka kyautata karatun shi kamar yadda ka ke yi a duniya; domin matsayinka na ƙarshe ita aya ta ƙarshe da za ka karanta”*. Imamu Ahmad a Musnad ɗinsa 2/192 da Abu Dawud a Sunan ɗinsa 1464, sannan Sheikh Albani ya intanga shi a Sahih al-Jaami’ 8122.

Mu hadu a fitowa ta 0️⃣5️⃣ in sha Allahu Ta’ala.

✍ Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*

===================================

Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar gizo a adireshinmu:-

Website:- www.fitila24.com

Ko ta waɗannan kafafan sadarwa:

YouTubeChannel:- Fitila24

Facebook Page:- Fitila24

Facebook Group:- Fitila24

WhatsApp:-07061639638

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:- Fitila24

Telegram channel:- Fitila24 Channel