August 5, 2020 By Adamu Abubakar 0

Gaskiya

HANYOYI GUDA TAMANIN (80) DA SUKE KUBATAR DA MUTUM DAGA WUTA*

Fitowa ta 0️⃣3️⃣

*GASKIYA*

Gaskiya ɗabi’a ce da take daukaka darajar mutum kuma ta nisanta shi daga  azabar wuta.

Allah Ta’ala Ya ce: *”Yaa ku wanda kuka yi imani, ku ji Tsoron Allah sannan ku kasance tare da masu gaskiya”* Sura al-Taubah 119.

Abdullahi bn Mas’ud, Radhiyallahu anhu, ya ce: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce:
*”Na hore ku da yin gaskiya, domin gaskiya tana shiryarwa zuwa ga nagarta, ita kuma nagarta ta na shiryarwa zuwa Aljanna. Kuma bawa ba zai gushe ba ya na yin gaskiya kuma yana kirdadon gaskiya har sai a rubuta shi mai gaskiya a wurin Allah…”*. Bukhari ya ruwaito 6094 da Muslim 105.

A wani hadisin wanda babban Sahabi, Abubakar al-Siddeeq, Radhiyallahu anhu, ya ce: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce:

*”Na hore ku da yin gaskiya domin yana tare da nagarta kuma duka su biyun suna Aljannah…”*. Bukhari ya fitar da hadisin a cikin al-Adabul Mufrad 724 da Ibn Maajah 3849.

Mu hadu a fitowa ta 0️⃣4️⃣ in sha Allahu Ta’ala.

✍ Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*

===================================

Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar gizo a adireshinmu:-

Website:- www.fitila24.com

Ko ta waɗannan kafafan sadarwa:

YouTubeChannel:- Fitila24

Facebook Page:- Fitila24

Facebook Group:- Fitila24

WhatsApp:-07061639638

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:- Fitila24

Telegram channel:- Fitila24 Channel