July 29, 2020 By Adamu Abubakar 0

Tsaida Sallar farilla kariya ce shiga daga wuta

Fitowa ta 0️⃣2️⃣

*KIYAYE SALLOLI BIYAR (5)*

Matsayi da daraja da amfanin sallah, ba abun da zai ambatu ba ne a irin wannan rubutu da ake so a yi shi a takaice, amma dai gare ka mai karatu:

Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce:
*”Mala’ika Jibril, ya zo mun daga Allah Ta’ala, sai ya ce: Yaa Muhammad, lallai Allah Ta’ala Yana cewa: Lallai na farlanta ma al’ummarka salloli guda biyar (5), don haka duk wanda ya cika su a cikin alwalansu da lokutansu kuma ya cika ruku’insu da sujadarsu, to yana da wani alkawari a wurin Allah na cewa zai shigar da su Aljanna a sanadiyar su. Kuma duk wanda ya hadu da Ni alhalin ya tauye wani abu daga cikin su, to ba shi da wani alkawari a wuriNa idan na ga dama in masa azaba, idan na ga dama in masa rahama*. A duba Sahih al-Jami’ 119 da Silsilatu ahaadith al-Sahihah 842.

Mu hadu a fitowa ta 0️⃣3️⃣ in sha Allahu Ta’ala.

✍ Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*

===================================

Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar gizo a adireshinmu:-

Website:- www.fitila24.com

Ko ta waɗannan kafafan sadarwa:

YouTubeChannel:- Fitila24

Facebook Page:- Fitila24

Facebook Group:- Fitila24

WhatsApp:-07061639638

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:- Fitila24

Telegram channel:- Fitila24 Channel