July 17, 2020 By Hassan Yusuf 0

YA ZA KI GANE DA GASKE YAKE SAN KI

BIRNIN MASOYA kashi na 6

Assalamu alaikum jama’a maza da mata. Barkarmu da sake haɗuwa a wannan gida na mu mai albarka, a kuma wannan shiri namu na BIRNIN MASOYA

Shirin BIRNIN MASOYA dai shiri ne da ke sharhi kan lamarin So da Soyayya da kuma Ƙauna …

Yau a cikin shirin namu za mu tattauna wani almari ne mai matukar mahimmanci, wato shine YA ZA KI GANE YANA SAN KI DA GASKE …

Kasancewar yadda samari ke amfani da harshensu wajan dabaibaye zuciyoyin ƴammata, ha anyar tattausan lafazi (sihirulkalam), mata da dama kan ruɗu su miƙa akalar zuciyarsu ba tare da haƙƙakewa ba, soyayya ta gaske ake musu, ko-kuwa soyayya ce ƙirƙirarriya da aka gina dan cimma wani buri, imma ga yarinyar kaitsaye ko ga ahalinta …

Wannan dalili ya sa wannan shiri zai haska mana wasu abubuwa da za su taimaka, wajan gane wanda ke sanki da gaske …

Daga cikin abin da za ki lura da shi akwai:
1. Zai baiyanar da soyayya:- zai rƙa baiyana soyayyar ki a fili ga jama’a.
2. Haɗaki za ƴan’uwansa:- zai yi ƙoƙarin haɗaki da ƴan’uwan shi, da baiyana ki a matsayin masoyiyarsa ko wacce zai aura.
3. Shiga cikin ƴan’uwanki:- zai baiyana kansa ga ƴan’uwanki, a matsayin masoyinki.
4. Tausayawa:- zai riƙa tausaya miki cikin lamuranki, tare da yunƙurin kawo miki ɗauki cikin lamuranki.
5. Ƙoƙarin fahimta:- zai yi ƙoƙari ya fahimci abinda kike so da wanda bakya so, dan tabbatar da shimfida ingantacciyar rayuwa mai cike da nashaɗi a tsakanin ku.
6. Yabawa:- zai riƙa yaban ki, musamman ɗabi’unki.
7. Sirri:- zai riƙa ɓoye aibinki tare da kokarin gyara miki, in kin yi kuskure.
Da dai suran abubuwa makamantan waɗannan

Za mu dakata a wannan gaɓa, sai in Allah Ya kaimu mako mai zuwa.

Amma kafin nan za mu amshi TSARABAR FITILA24 daga BIRNIN MASOYA:-
Ba abin da na rasa a soyayya
Ni ina da kai a rayuwata sai jinya
Kallan da kake min yake sani jin kunya
Da kyawawan idanuwanka masu kyau da tozali…..

A madadin ɗaukacin mahukunta kafar Fitila24 Ni da na shirya na gabatar Hassan Yusuf Fitila, muke muku fatan alheri. Mu tara amai mai zuwa dan jin mu da wani saban shirin.
Bissalam

**********
Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar-gizo (Intanet) a adireshinmu:- www.fitila24.com

Ko ku biyo mu ta wannan links ɗin:

Facebook Page:- https://m.facebook.com/fitila24/

Facebook Group:- https://m.facebook.com/groups/327058064166378?refid=27

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:-
https://t.me/joinchat/MZdkwxYWzIgTCQg7gWoO_w

WhatsApp:-07061639638

===================================

Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar gizo a adireshinmu:-

Website:- www.fitila24.com

Ko ta waɗannan kafafan sadarwa:

YouTubeChannel:- Fitila24

Facebook Page:- Fitila24

Facebook Group:- Fitila24

WhatsApp:-07061639638

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:- Fitila24

Telegram channel:- Fitila24 Channel