July 7, 2020 By Adamu Abubakar 0

Anyar kubuta daga wuta 1

HANYOYI GUDA TAMANIN (80) DA SUKE KUBATAR DA MUTUM DAGA WUTA

Fitowa ta 0️⃣1️⃣

TAUHIDI

Al’amarin Aqida abu ne wanda ba shi da na biyu, domin akan shi ne addini yake ginuwa gaba dayan shi.

Kuma Allah Ta’ala, ba Ya karban aikin mutane har sai idan Aqidarsu ta yi kyau.

Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya fada a cikin hadisin Qudusi daga hadisin Anas Ɗan Malik, Allah Ta’ala Ya ce:

*… “Ya kai ɗan adam inda zaka zo Mun da kwatankwacin kasa na zunubai sannan ka haɗu da Ni ba ka shirka dani ba ko ɗaya, da Na zo maka da makamancin ta na gafara”*. Al-Tirmizi ya fitar da hadisin 3540.

*MA’ABOTA TAUHIDI, SU NE WANDA ZA SU DACE da6 CETON MANZON ALLAH, SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAMA.*

Abi Hurairah, Radhiyallahu anhu, ya ce: Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce:
*”Kowane Annabi ya na da addu’ar da ake amsa masa; sai kowanne ya gaggauto da addu’ar shi, amma Ni na tanaji addu’ata ta kasance ceto ga al’ummata ranar al-Qiyamah kuma za ta samu ne da yardan Allah ga dukkan wanda ya mutu daga cikin al’umma ta alhalin ba ya shirka”*. Muslim ya riwaito 199.

Yaa Allah Kar ka haramta mana ni’imar tauhidi kuma Ka tashe mu cikin tawagar masu kadaita Ka tare da Shugaban masu Tauhidi, sallallahu alaihi wa sallama.

Mu hadu a fitowa ta 0️⃣2️⃣ in sha Allahu Ta’ala.

✍ Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*

===================================

Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar gizo a adireshinmu:-

Website:- www.fitila24.com

Ko ta waɗannan kafafan sadarwa:

YouTubeChannel:- Fitila24

Facebook Page:- Fitila24

Facebook Group:- Fitila24

WhatsApp:-07061639638

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:- Fitila24

Telegram channel:- Fitila24 Channel