May 29, 2020 By Adamu Abubakar 0

Hakan ba al’adarmu ba ce

Lallai addininmu (MUSULUNCI) ya shiryar da mu yin soyayya da baiyana ta, da kuma aikata ta.

A ɓangare guda kuma ya nuna mana kunya, ya kwaɗaitar da mu ita kuma ya mana matsayin ta.

A ƴan kwanakin nan, wasu clips na videos suna yawo in da za ka ga ƙaton gardi, da wata su na rawa cikin rashin kunya da sunan nuna soyayya.

To mu sani irin wannan mummunar ɗabi’a ta saɓawa sunnar Baban Alƙasim S.A.W kuma ta saɓawa tsamtatacciyar tarbiyyar al’adar da mu ka gada Iyayanmu a ƙasar Hausa.

Da haka muke kira ga jama’a da a guji haɗawa da yaɗa irin waɗannan videos, do min yin hakan ba daidai bane, saɓawa Allah ne, da ƙokarin kwaikwayon kafirai ko futsararru.

Wasu kan yaɗa irin videos ɗin a babin Nishaɗi, to mu sani ba a wargi da ƙa’idojin Ubangiji, kuma meye ribarka, kasa mutane nishaɗi/dariya kai kuma ka tashi da tarin zunubi?

Allah Ya kyauta, Allah Ya shiryemu baki daya 🤲

Bissalam🙏

®_Hassan Yusuf Fitila

===================================

Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar gizo a adireshinmu:-

Website:- www.fitila24.com

Ko ta waɗannan kafafan sadarwa:

YouTubeChannel:- Fitila24

Facebook Page:- Fitila24

Facebook Group:- Fitila24

WhatsApp:-07061639638

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:- Fitila24

Telegram channel:- Fitila24 Channel