May 16, 2020 By Adamu Abubakar 0

Daga Malamanmu

DARASI DAGA RAYUWAN UWA DA DANTA

Al-fudhail Bn ‘Iyaadh, Rahimahullah, ya ce: Na koyi Darasi daga rayuwar karamin yaro. Wata rana na zo zan wuce zuwa Masallaci, sai na ji wata mata tana dukan danta daga cikin gida yana ihu, sai wannan yaro ya bude kofa ya fito ya gudu sai mahaifiyar ta mayar da kofa ta rufe.

Lokacin da na dawo daga Masallaci sai na ga yaron nan bayan ya yi kuka kadan sai ya dawo bakin kofa yana lallashin Mahaifiyar shi har sai da ya kwanta har bacci ya dauke shi a wurin. Ganin haka sai mahaifiyar ta bude masa kofa ya shiga.

Ganin abun da ya faru sai Al-fudhail Bn ‘Iyaadh, Rahimahullah, ya fashe da kuka, ya ce: TSARKI YA TABBATA GA ALLAH!, INDA BAWA ZAI YI HAKURI A KOFAN ALLAH, DA ALLAH TA’ALA YA BUDE MASA

A duba littafin المصنف na Ibn Abiy Shaibah 6/22.

✍🏼 Dan uwanku a Musulunci:malam
Umar Shehu Zaria

===================================

Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar gizo a adireshinmu:-

Website:- www.fitila24.com

Ko ta waɗannan kafafan sadarwa:

YouTubeChannel:- Fitila24

Facebook Page:- Fitila24

Facebook Group:- Fitila24

WhatsApp:-07061639638

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:- Fitila24

Telegram channel:- Fitila24 Channel