April 20, 2020 By Adamu Abubakar 0

IBADUN MANZON ALLAH A WATAN RAMADAN

FITOWA TA 3:

Kuma a wani hadisin cewa ya yi: “Sau da yawa akan samu mai azumi, ba shi da wani rabo a azuminsa face yunwa da kishin ruwa”. Imamu Ahmad da Ibn Hibban suka riwaito kuma Imamu Assiyudiy ya inganta shi.

Abin da hadisin ya ke nufi shi ne, mai aikata wannan ba shi da ladan azumi, domin ya keta alfarman azuminsa ta sanadin aikata sabon Allah da abin da shari’a ta hana, wannan ne ma ya sanya wani daga cikin magabata ya ce: mafi kaskancin azumi, shi ne azumin da kawai mai yin sa kamewa ya yi ga barin cin abinci da abun sha.

Hakika Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya bayyana mana azumi na gaskiya kariya ne daga dukkan wani aiki abun zargi da dabi’u marasa amfani. Domin ya ce: “Azumi garkuwa ne, don haka idan ranar azumin dayan ku ya kasance, to Kar ya yi jima’i ko maganganun batsa, kuma kar ya yi fasikanci, koda wani ya zage shi ko ya nemi fada da shi, to ya ce: lallai ni ina azumi, lallai ni ina azumi”. Bukhari da Muslim ne suka riwaito.

Wannan shi ne irin azumin da ake bukata daga dukkan Musulmi, kuma shi ne azumin da zai Kai ma’abocinsa zuwa ga fadin Allah Ta’ala: “Ya ku wadanda kuka bada gaskiya, an wajabta azumi a kanku, kamar yanda aka wajabta a kan wadanda suka gabace ku, (an yi haka ne) don ku ji tsoron (Allah). suratul Baqarah 183.

NA BIYU: TSAYUWAR SALLAH A WATAN RAMADAN:

Hakika Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana tsayuwa sallan dare a tsahon shekara, ya na mai riko da fadin Allah Ta’ala: “Ya Kai wannan mai lullube wa! Ka raya dare sai dan kadan (daga cikinsa). Suratul Muzammil aya ta 1 da ta 2.

Kuma hakika Allah Ta’ala, Ya yabi masu tsayuwa su na Sallah cikin dare, inda yake cewa:” (Su ne) kuma masu kwana suna sujjada da kiyamullaili saboda Ubangijinsu”. Suratul Furqan aya ta 64.

Sannan ya Kara cewa: “kirajansu suna nisantar wararen kwanciya, suna bauta wa Ubangijinsu, suna masu tsoro da kuma kwadayi, kuma suna ciyarwa daga abin da Muka azurta su”. Suratus Sajadah aya ta 16.

Kamar yanda a wani hadisi yake cewa:” Mafi darajan Sallah bayan sallar, farilla, ita ce sallan dare”. Muslim ne ya ruwaito.

Hakika ya tabbata Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya na kebance tsahuwar sallan Ramadan da wani irin himma wanda ba ya kebance wani watan da shi, don haka ne ma ya kwadaitar da tsayuwan Sallah a watan Ramadan……

Mu hadu a fitowa ta 4 in sha Allahu Ta’ala.

✍🏼 Dan uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria
09/06/2015

===================================

Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar gizo a adireshinmu:-

Website:- www.fitila24.com

Ko ta waɗannan kafafan sadarwa:

YouTubeChannel:- Fitila24

Facebook Page:- Fitila24

Facebook Group:- Fitila24

WhatsApp:-07061639638

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:- Fitila24

Telegram channel:- Fitila24 Channel