April 18, 2020 By Adamu Abubakar 0

IBADUN MANZON ALLAH A WATAN RAMADAN

FITOWA TA 2:

Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya gargade mu akan yin sakaci da barin wannan wata ya wuce ba tare da mun ribaci darajan da ke cikin sa ba, kuma ya nuna mana kada mu yarda wannan wata ya fita ba tare da an gafarta mana zunubanmu ba, an kuma daga darajarmu a wurin Allah.

An karbo daga Abi Hurairah, Allah Ta’ala Ya kara yarda a gare shi, cewa lallai Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya taka minbari ya hau sai ya ce: “Amin, amin, amin”, sai aka ce: Yaa Manzon Allah! Ka hau minbari sai muka ji ka ce: “amin, amin, amin”.

Sai ya ce: “Lallai Mala’ika Jibril ne, amincin Allah su tabbata a gare shi, ya zo mun, sai ya ce:” Duk wanda ya riski watan Ramadan, kuma ba a gafarta masa ba, har ya shiga wuta, to Allah Ya kara nisanta shi, ka ce: amin. Sai na ce: amin”. Ibn Khuzaimah da Ibn Hibban suka riwaito, kuma Sheikh Nasiriddeen Albani ya ce hadisi ne mai kyau ingantacce.

Don haka, abin da ya cancanci dukkan wani Musulmi shi ne, ya kiyaye tozarta lokacinsa a cikin wannan wata, tun daga aikata abin da zai fusata Allah Ta’ala, ko ma aikata abubuwan da suka halasta, amma babu lada a cikin aikata su, domin wanda ya munana ayyukansa a gidan Duniya, idan ya ga wanda suka kyautata ranar alqiyamah zai yi nadama, ko kuma ya yi kuka na bakin ciki da radadi.

Hakika Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya bamu labarin cewa akwai daga cikin mutane wanda yake azumi na al’ada, don haka azumi ba shi da wani tasiri wajen gyara dabi’unsa, ko tsaftace furucinsa, ta yanda za ka ga Mutum bai dauki azumi a matsayin komai ba face kawai kamewa ga barin cin abinci, wannan shi wanda Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ke magana dangane da su, ya ke cewa: “Duk wanda bai bar maganar karya da aiki da shi, da jahilci, to Allah Ba shi da bukatar ya bar abincinsa da abin shansa”. Bukhari da Muslim ne suka riwaito.

Kuma a wani hadisin cewa ya yi: “Sau da yawa akan samu mai azumi, ba shi da wani rabo a azuminsa face yunwa da kishin ruwa”. Imamu Ahmad da Ibn Hibban suka riwaito kuma Imamu Assiyudiy ya inganta shi.

Abin da hadisin ya ke nufi shi ne….

Mu hadu a fitowa ta 3 in sha Allahu Ta’ala.

✍🏼 Dan Uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria
08/06/2020

===================================

Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar gizo a adireshinmu:-

Website:- www.fitila24.com

Ko ta waɗannan kafafan sadarwa:

YouTubeChannel:- Fitila24

Facebook Page:- Fitila24

Facebook Group:- Fitila24

WhatsApp:-07061639638

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:- Fitila24

Telegram channel:- Fitila24 Channel