April 17, 2020 By Adamu Abubakar 0

IBADUN MANZON ALLAH A WATAN RAMADAN

IBADUN MANZON ALLAH A WATAN RAMADAN

FITOWA TA 1:

Dukkan yabo da jinjina da kirari sun tabbata ga Allâh Ta’ala, Sarkin da bai haifa ba kuma ba a haife shi, sannan ba shi da abokin tarayya. Tsira da amincin Allah su tabbata ga ManzonSa, wanda aka aiko shi rahama ga Talikai.

Bayan haka, yan uwa duba da yanda Allah Ta’ala Ya ara mana tsahon kwana har muka kawo wannan lokaci da ake gab da shiga watan Ramadan a daidai lokacin da bara mun yi Azumi da wasu amma Allah Ta’ala Ya karbi rayuwansu ba don an yi musu garaje ba, mu kuma aka bamu aron numfashi, ba don wata rana mu ma ba za mu mutu ba, ya sanya na ga ya dace in tunatar da Kaina sannan yan uwana dangane da yanda Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ke ibada a watan Ramadan, domin mun sani dukkan mai neman tsira to dole ya yi riko da tafarkin da ya rayu akai.

Kamar yanda muka sani watan Ramadan wata ne na ibada, biyayya da neman kusanci zuwa ga Allah Ta’ala ta hanyan ibadu da dama da kuma dagewa wajen ayyukan da’a. Kuma ya kasance daga shiriyar Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya na yawaita ibada a watan Ramadan, kuma ya na kebance shi da wasu ibadu wanda ba ya kebance wani wata da irin sa. Sannan kuma ya na kadaitar da Sahabbansa da su fuskanci Allah gadan-gadan a wannan wata, domin an samu ya na cewa: “Idan daren farkon watan Ramadan ya shiga, ana daure shaidanu, da Aljannu masu taurin kai, kuma a rufe kofofin wuta, ta yanda babu wani kofa nata da za a bude, kuma a bude kofofin Aljannah, ta yanda babu wani kofa nata da zai saura a rufe, kuma mai kira zai yi kira a kowane dare, Yaa Kai mai kwadayin alheri ka fuskanci, kuma yaa Kai mai kwadayin sharri ka takaita, kuma Allah Ta’ala Ya na da wasu bayi da ya ke ‘yantawa daga wuta, kuma wannan ya na faruwa a kowane dare”. Imamul Bukhari da Muslim suka ruwaito.

YANA DAGA CIKIN IBADUN ANNABI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI A WATAN RAMADAN:

NA FARKO: AZUMTAN WATAN RAMADAN:

Allâh Ta’ala Ya na cewa: “Dukkan wanda ya shaida watan to ya azumce shi”. Suratul Baqarah 185.

Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Dukkan wanda ya azumci watan Ramadan, ya na mai Imani kuma mai neman lada a wurin Allah, to an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”. Bukhari da Muslim ne suka riwaito.

Haka nan Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Ga watan Ramadan nan ya zo muku, wata mai albarka, Allah Ta’ala Ya wajabta muku azumtan shi”. Nasa’i ya ruwaito, Malam Albani ya inganta shi da wanin shi.

Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya gargade mu akan yin sakaci da barin wannan wata ya wuce ba tare da mun ribaci darajan da ke cikin sa ba……

Mu hadu a fitowa ta 2 in sha Allahu Ta’ala.

✍🏼 Dan Uwanku a Musulunci:
Umar Shehu Zaria
08/06/2015

===================================

Domin samun kayatattun shirye-shiryan FITILA24 sai ku ziyarcemu a babban shafinmu a yanar gizo a adireshinmu:-

Website:- www.fitila24.com

Ko ta waɗannan kafafan sadarwa:

YouTubeChannel:- Fitila24

Facebook Page:- Fitila24

Facebook Group:- Fitila24

WhatsApp:-07061639638

Twitter:- @Fitila24

Telegram Group:- Fitila24

Telegram channel:- Fitila24 Channel